
11.7K
XCRanar Jumu'a misalin karfe 7:30 na safe, mutane na shirin zuwa masallacin Idi. Sai ga wani bawan Allah yazo da Akuya; rai ga hannun Allah. Yana neman a duba mai ita.
Bayan tambayoyin dana masa da kuma "examining" Akuyar a Ilimance, na gano cewa haihuwa ce kuma ba zata iya haihuwar da kan ta ba.
Nayimishi bayanin dole sai anyi mata tiyata (C.S) domin a cire abunda ke ciki.
Tareda taimakon wasu "Corpers" da suke asibitin mu, na ciremata 'Da, namiji, matacce wanda har ya fara kumbura.
Muka gama aikin cikin sauri sannan na rubuta mishi maganin da zai saye da za'a ci gaba da kula da ita har tsawon sati daya da 'yan kwanaki.
Yau kwana na biyar kenan da aikin. Ana samun ci gaba sosai a lafiyar ta. Allah ya qara mata lafiya. Amin.
Rahoto daga asibitin dabbobin da ke garin Dalijan, Gwandu, Kebbi State.
#ZakeeJr.
@xclusive_people










